Lahadi 5 Yuli 2026 - 14:05
Al'ummar Musulmi Su Sauke Nauyinsu Na Daukar Fansar Jinin Shahidin Jagora / Riko Da Wilayatul Faƙih Wajibi Ne 

Hauza/ Ayatullah al-Uzma Makarem Shirazi, yayin da yake jaddada nauyin da ya rataya a wuyan al'ummar Musulmi na daukar fansar jinin Shahidin jagora, ya bayyana cewa: "Masu kisan da kuma wadanda suka aikata wannan babban laifi, wadanda hannayensu suka cuɗanya da jinin wannan shahidi mai girma, kwamandoji, jami'ai, mutane marasa kariya da yara marasa laifi, ba za su tsira daga azabar Allah da hukuncin adalci ba, kuma al'ummar Musulmi za ta ci gaba da sauke nauyinta na neman fansar jinin wadannan shahidai a cikin iyakokin shari'a da doka."

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana a cikin wani sako, yayin da yake jaddada muhimmancin halartar jama'a da yawa a taron bankwana da jana'izar Shahidin jagoran juyin juya halin Musulunci, cewa: "Yaƙi bai ƙare ba, saboda haka duk wani ƙoƙarin yaɗa yanke ƙauna, kasala, toshewar hanya da raunana gwiwar jama'a, jami'ai da dakarun tsaro yana tafiya ne da muradin maƙiyi kuma ya saɓa wa muradun ƙasa da al'ummar Musulmi.

Wannan marja'in ya kuma jaddada batun neman adalci kan jinin Shahidin jagora, inda ya bayyana cewa: "Masu kisan da kuma wadanda suka aikata wannan babban laifi, wadanda hannayensu suka cuɗanya da jinin wannan shahidi mai girma, kwamandoji, jami'ai, mutane marasa kariya da yara marasa laifi, ba za su tsira daga azabar Allah da hukuncin adalci ba, kuma al'ummar Musulmi za ta ci gaba da sauke nauyinta na neman adalci kan fansar jinin wadannan shahidai a cikin iyakokin shari'a da doka."

Riko da Wilayatul Faƙih yana daga cikin muhimman batutuwan sakon Ayatullah Makarem Shirazi. A wannan bangaren ya rubuta cewa: "Juyin Juya Halin Musulunci ya ginu ne a kan asasin Wilayatul Faƙih mai daraja, kuma da albarkacin wannan asasi ne aka tsallake mawuyacin hali da makircin maƙiya masu yawa. Wilayatul Faƙih a tsarin Musulunci ita ce ginshikin haɗin kai, mai kare muradun al'umma kuma ginshiƙi mai ƙarfi na tsarin, kuma riko da ita wajibi ne ga kowa kuma hanya ce ta kare Musulunci da ƙasa."

Cikakken saƙon Ayatullah Makarem Shirazi kamar haka yake:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

"Lalle ne mu daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma."

A daidai lokacin da ake gudanar da bankwana da jana'izar tsarkakakken gangar jikin Shahidin jagoran juyin juya hali, baƙin cikin rashin wannan gwarzon mai hikima ya sake zama sabo. Babu shakka, halartar jama'a da yawa a wannan taro wata alama ce ta ƙarfi da biyayya ga manyan manufofin Juyin Juya Halin Musulunci, kuma shaida ce ta tsayin dakan al'umma mai girma ta Iran da al'ummar Musulmi da kuma ci gaba da tafarkin shahidai.

A cikin wannan yanayi, ya zama dole a kula da wasu batutuwa:

Na farko: Bai kamata a ɗauka cewa wannan yaƙi ya ƙare ba; a'a, gwagwarmaya da sansanin masu girman kai tana ci gaba. Saboda haka, duk wani ƙoƙarin yaɗa yanke ƙauna, kasala, toshewar hanya da raunana gwiwar jama'a, jami'ai da dakarun tsaro yana tafiya ne da muradin maƙiyi kuma ya saɓa wa muradun ƙasa da al'ummar Musulmi. Hakika, bege da juriya ba su nufin yin watsi da haƙiƙanin yanayin da ake ciki ba; a'a, haƙuri da juriya suna daga cikin manyan abubuwan samun nasara a jarabawar Ubangiji.

Na biyu: Masu kisan da kuma wadanda suka aikata wannan babban laifi, wadanda hannayensu suka cuɗanya da jinin wannan shahidi mai girma, kwamandoji, jami'ai, mutane marasa kariya da yara marasa laifi, ba za su tsira daga azabar Allah da hukuncin adalci ba, kuma ba za a taɓa mantawa da wannan jini mai tsarki ba. Al'ummar Musulmi za ta ci gaba da sauke nauyinta na neman adalci kan fansar jinin wadannan shahidai a cikin iyakokin shari'a da doka.

Na uku: Jami'ai, dakarun tsaro da duk masu yanke shawara su dogara ga Allah Maɗaukaki, su amince da alkawuran Allah, su yi amfani da dukkan damar da ƙasa take da ita, kuma su dogara da imani, haƙuri da juriyar jama'a, tare da tsari, ƙarfi da taka-tsantsan, a fagen soja, diflomasiyya da sauran fannoni, su tsaya tsayin daka a gaban maƙiyi; domin ƙwarewa ta nuna cewa duk wani ja da baya a gaban maƙiyi mai cin zarafi yana ƙara masa ƙarfin guiwa wajen ci gaba da cin zarafi da kwaɗayi.

Na huɗu: Juyin Juya Halin Musulunci ya ginu ne a kan asasin Wilayatul Faƙih mai daraja, kuma da albarkacin wannan asasi ne aka tsallake mawuyacin hali da makirce-makircen maƙiya masu yawa. Wilayatul Faƙih a tsarin Musulunci ita ce ginshikin haɗin kai, mai kare muradun al'umma kuma ginshiƙi mai ƙarfi na tsarin, kuma riko da ita wajibi ne ga kowa kuma hanya ce ta kare Musulunci da ƙasa.

Na biyar: A yau fiye da kowane lokaci, kiyaye haɗin kai da dunkulewar ƙasa wajibi ne da ba za a iya musantawa ba. Bai kamata bambancin ra'ayi ba, ko da kuwa ya samo asali ne daga kyakkyawar manufa, ya zama sanadin rarrabuwar kai da raunana a cikin gida. A lokaci guda kuma, ya kamata jami'ai masu daraja su ƙara himma wajen magance matsalolin jama'a da yi musu hidima cikin gaskiya.

Ina sake miƙa ta'aziyyata ta shahadar wannan masoyi da sauran shahidan wannan yaƙin da aka ɗora mana, zuwa ga gaban Mai Martaba Baƙiyyatullah al-A'azam (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), Jagoran Juyin Juya Hali mai girma, iyalan shahidai, al'umma mai daraja ta Iran da daukacin Musulman duniya. Ina roƙon Allah Maɗaukaki Ya ɗaukaka darajojinsu, kuma ina fatan cikin inuwar kulawar Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), ɗaukaka da nasarar Musulunci da Musulmi da kawar da sharrin maƙiya su tabbata cikin gaggawa.

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu

Qum – Naser Makarem Shirazi

14 Tir 1405 (5 ga Yuli 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha